9 Satumba 2020 - 10:42
Ministan Harkokin Wajen Indiya Na Ziyara A Iran

Ministan harkokin wajen kasar Indiya, ya fara wata ziyarar aiki yau Talata a birnin Tehran.

ABNA24 : Yayin ziyarar tasa Subrahmanyam Jaishankar, ya tattauna da takwaransa na Iran, Mohammad Javad Zarif.

Bangarorin sun tattauna kan batutuwa da dama, da suka shafi alakar dake tsakaninsu.

Ziyarar ta ministan, na zuwa ne bayan wacce ministan tsaron kasar ta Indiya, ya kawo shi ma a nan Tehran kwanaki biyu da suka wuce.

Kasashen Iran da Indiya dai na da dadaddiyar alaka a tsakaninsu.

342/